Kwayet yana baka damar lura da kasuwancinka kai tsaye. Kula da tallace-tallace, kaya, kuɗi, da riba cikin sauƙi. Yana sanar da kai komai game da harkokinka, ko'ina kake. Cikakke ga kowane irin kasuwanci.
Kwayet na kawo sabon salo wajen gudanar da kasuwancinka, yana baka damar ganin duk abin da ke faruwa a cikin ainihin lokaci, duk inda kake a fadin duniya. Zaka iya gane cikakhen bayani kan wanene ya sayar, menene aka sayar, yaushe, da kuma daga wane wuri, kamar kana wurin. Bugu da kari, Kwayet zai sanar da kai nan take idan aka samu wani motsi ko aiki da ba a yarda da shi ba, tare da tunasarwa game da karancin haja kafin ta kare gaba daya, domin ka cike ta a kan lokaci ba tare da wata tsaiko ba. Wannan yana baka damar sarrafa kasuwancinka da nutsuwa, ko daga gida, ko daga tafiya.
Ta bangaren kudi, Kwayet ya sanya bibiyar riba da kashe-kashenka cikin sauki marar misaltuwa. Zaka iya fahimtar adadin kudin da kake samu a zahiri, tare da sanin tushen shigowarsa, ko ta hanyar tsabar kudi ne, POS, ko canja wuri ta banki. Kwayet yana baka damar duba ribarka ta yau, ta mako, ta wata, har ma da na shekara, tare da sanin abin da ya rage a asusunka a kowane lokaci. Wannan cikakkiyar hangen nesa kan harkokin kudin kasuwancinka zai baka damar yanke shawara mai inganci da kuma shiri na gaba.
Ko menene irin kasuwancinka, Kwayet kayan aiki ne da zai canza salon gudanarwarka. Daga shaguna kanana da manya, manyan kantuna (supermarkets), otel-otel, makarantu, gidajen abinci, asibitoci, har zuwa ofisoshi, Kwayet ya dace da kowane bangare kuma an gina shi don biyan bukatun kasuwancin zamani. Yana kawo tsari, daidaito, da kuma natsuwa ga masu kasuwanci ta hanyar samar da ingantattun bayanan da ake bukata.